Kungiyar Mabiya Mazhabar Shi’a ta Najeriya (IMN) a ranar Juma’a ta gudanar da tattakin nuna goyon bayanta ga Falasdinawa a daidai lokacin da kasar Isra’ila ke ci gaba da kai musu hare-hare a Zirin Gaza.
An gudanar da tattakin na luma ne bayan idar da sallar Juma’a a Masallacin Kasa da ke Abuja.
- Za a yi wa ’yan mata miliyan 7 rigakafin cutar kansar mahaifa a Najeriya
- An sa zare tsakanin Rarara da mutanen Buhari
A cikin wata sanarwa, daya daga cikin mambobin kungiyar, Sheikh Sidi Munir Sokoto, ya bukaci ’yan Najeriya da su tallafa wa Falasdinawa kan abin da ya kira danniyar da suke fuskanta daga Yahudawan Isra’ila.
Ya ce, “Falasdinawa da ke dukkan fadin kasar Faladinu na ci gaba da shan wahala saboda kisan kiyashin da ake yi musu da kuma wahalhalun da suke ciki.
“Asibitoci sun koma kangwaye saboda babu kayan aiki babu magunguna, babu wuta, babu ruwa. Yahudawa sun kirkiri bala’in da zai iya ɗaiɗaita kusan mutum miliyan 2.2.
“Rahin imani da tausayi ne mu koma mu nade hannuwanmu muna kallo, akalla za mu iya gudanar da zanga-zanga mu nuna bacin ranmu da wannan rashin adalcin. Mun kuduri aniyar yin wannan tattakin daga Masallacin Kasa zuwa unguwar Wuse, amma jami’an tsaro suka dakile mu, ya kamata mu taimaka wa wadannan mutanen da ake kokarin dannewa,” in ji Sheikh Sidi.