Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta ceto mutum 18 daga hannun ’yan bindiga da suka yi yunƙurin garkuwa da su a hanyar Funtua zuwa Gusau.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq, ya fitar.
- ’Yan sanda sun kama matar da ta jefar da jaririnta a gefen hanya
- ’Yan bindiga sun kashe sojojin kamaru 6 a kan iyakar Najeriya
Ya bayyana cewa ’yan sandan sun daƙile harin tare da ceto mutanen, bayan wasu huɗu sun ji rauni.
Hakazalika, ’yan sandan sun samu nasarar daƙile wani hari da ‘yan bindiga suka kai Gidan Gada, a Ƙaramar Hukumar Kafur, inda suka sace shanu.
Kakakin ’yan sandan yankin Kafur da Malumfashi ya jagoranci tawagarsa, inda suka bi sahun ’yan bindigar zuwa ƙauyen Fanisau, inda aka yi musayar wuta kuma aka ceto dukkanin dabbobin da suka sace.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Aliyu Abubakar Musa, ya jinjina wa jami’an kan wannan nasara.
Ya buƙaci al’umma su ƙara bai wa jami’an tsaro goyon baya da kuma bayar da bayanai da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankunansu.