’Yan sandan Isra’ila sun tarwatsa wasu Falasdinawa masu zanga-zanga kan ci gaba da korarsu tare da rusa musu gidaje da suke zargin kasar da yi a gabar Yammacin Kogin Jordan.
Falasdinawan dai na zanga-zangar ne a yankin Sheikh Jarrah da ke gabashin birnin Kudus ranar Juma’a.
- Kwankwasiyya kamar kungiyar asiri ce –Kwankwaso
- ‘Kwararrun likitocin kwakwalwa dubu 10 ke aiki a kasashen waje’
Ko a watan Mayun bara dai sai da tarzoma ta barke a yankin na Sheikh Jarrah bayan Isra’ila ta tashi daruruwan Falasdinawa daga muhallansu.
A birnin Kudus dai, Falasdinawa da dama ne suka shimfida daddumu suka gudanar da sallolin rokon Allah, kafin daga bisani su wuce don yin zanga-zanga.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya rawaito cewa ’yan sandan Isra’ilan da ke gadin kan iyakar kasar sun yi amfani da dawakai wajen tarwatsa masu zanga-zangar bayan sun toshe hanyoyi.
’Yan sandan dai sun bayyana zanga-zangar a matsayin tayar da zaune tsaye, inda suka ce mutanen sun ki bin umarnin ’yan sanda.
Wakilin kamfanin AFP ya lura cewa an daddaure mutum biyu, ko da yake ’yan sandan sun ce ba su kama kowa ba.
Yankin na Sheikh Jarrah dai ya kasance wani wurin da ake gumurzu tsakanin Yahudawan da Falasdinawa.
Isra’ila dai ta kwace Gabashin birnin Kudus ne daga kasar Jordan a shekarar 1967 bayan wani yakin kwana shida da aka yi, ko da yake hukumomin kasa da kasa sun ki amincewa da matakin.
Sama da Yahudawa 200,000 ne ke zaune a Gabashin birnin na Kudus, wanda Falasdinawan ke cewa nan ne halastaccen babban birninsu.