Akalla Falasdinawa 42 ne aka tabbatar ’yan sandan Isra’ila sun jikkata a masallacin birnin Kudus lokacin da suke ibada a Juma’ar karshe ta watan Ramadan.
Kungiyar ba da agaji ta Red Crescent a kasar ta ce harin na zuwa ne bayan shafe tsawon makonni Isra’ilar na kai hari kan Falasdinawan.
- Masu kwacen waya sun raunata ma’aikaciyar Daily Trust a Kano
- A fara duban watan Sallah daga ranar Asabar – Sarkin Musulmi
Isra’ila dai ta ce dakarunta sun shiga harabar masallacin ne bayan ta zargi masa zanga-zanga da jefa duwatsu a wajen ibadar Yahudawa na Western Wall mai tsarki da ke kusa da masallacin.
Wasu ganau sun ce ’yan sandan dai sun harba barkonon tsohuwa ne tare da yi harbi da harsasan roba a kan masu ibada.
Isra’ila dai ta ce ta kama mutum uku bisa zargin jifa da duwatsun a kan Yahudawan masu ibada.
Sama da mako biyu ke nan ana zaman dar-dar tsakanin Falasdinawa da Yahudawa a yankin.
Kusan cikin wata daya da wuce, sama da Falasdinawa 300 ne aka jikkata a masallacin, wanda ke zama na uku mafi tsarki ga Musulmai a duniya.
Harin dai na ranar Juma’a na zuwa ne yayin da Musulmai ke kokarin karkare azumin watan Ramadan a karshen makon nan.