✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda za su yi wa motoci rajista da fasahar zamani a Nijeriya

Rundunar ta ce daga ranar 29 ga watan Yulin 2024, sabon tsarin mai amfani da na’urorin zamani.

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa za ta fara amfani da fasahar zamani wajen yi wa motoci a ƙasar nan rajista nan da kwana 14.

Rundunar ta ce daga ranar 29 ga watan Yulin 2024, sabon tsarin mai amfani da na’urorin zamani, zai fara aiki domin inganta tsaro a sassan ƙasar.

Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Asabar ɗin.

Adejobi ya ce sabon tsarin da Babban Sufeton ’Yan sanda Kayode Egbetokun ya kawo na da nufin daƙile matsalar tsaro kama daga satar ababen hawa da fashi da makami.

Ya ce tsarin rajistar motocin wanda aka yi wa laƙabi da e-CMR zai taimaka wajen inganta aikin jami’an ’yan sanda wajen gudanar da bincike da daƙile aikata laifuka ta amfani da ababen hawa, har ma da ayyukan ’yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya.

Sanarwar ta ce sabon tsarin rijistar ababen hawan zai riƙa amfani da fasahar zamani wajen tattara bayanan kai tsaye na ababen hawa da waɗanda suka mallake su da kuma ayyukan da suke yi da su.

Hakan na nufin daga lokacin fara aiki da wannan sabon tsari, duk wasu sauye-sauye na takardun mota ko kuma wasu sassan motar za su gudana cikin sauƙi ba kamar yadda a baya ake ɗaukar lokacin haɗa irin waɗannan takardu ba.