Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta tsare jigon jam’iyyar NNPP, Aliyu Madaki bisa fita yawon yakin neman zabe da bindiga.
Madaki, wanda Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ayyana a matsayin zababben dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Dala a farkon makon nan, ana zargin shi da fita da bindiga lokacin da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya isa jihar don rufe yakin neman zabensa a jihar.
Akalla mutum bakwai ne rahotanni suka ce sun mutu, an kuma ce an kone motoci da wasu kadarori a rikicin da ya barke lokacin da wasu ‘yan banga suka farmaki magoya bayan jam’iyyar NNPP a kan hanyarsu ta tarbar Kwankwaso.
Wata majiya a jam’iyyar NNPP da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da cewa, ‘yan sanda sun gayyaci Madaki a yau [Laraba] kuma an yi masa tambayoyi kan hotunan da suka karade kafafen sada zumunta.
Majiyar ta ce Madaki ya gabatar da lasisin mallakar bindigarsa ga jami’an tsaron.
Sai dai majiyar ba ta tabbatar da ko an tsare jigon na NNPP ba.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar da cewa an gayyaci Madaki bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ka’ida ba.
Ya kara da cewa, “yanzu haka yana tare da mu a CID kuma ana ci gaba da bincike.”