✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun watsa casun tsiraici a Adamawa

An shirya gudanar da casun tsiraicin ne a bakin wani kogi

’Yan Sanda sun dakile wani casun tsiraici da aka shirya gudanarwa a bakin wani kogi a Jihar Adamawa.

Rundunar ’Yan Sandan ta dauki matakin ne bayan mazauna sun kai mata korafi kan casun na tsiraici da ake zargin wasu matasa sun shirya gudanarwa a Yola, babban birnin Jihar.

Sanarwar dabdalar mai suna ‘Yola Beach Party’, wadda aka shirya gudanarwa a ranar Lahadi ta karade shafukan sada zumunta.

Sanarwar ta ce mahalarta za su biya N2,000 kudin shiga, sai dai ba ta bayyana wurin da za a sheke ayar ba.

Tuni dai Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya ba da umuarnin a binciki lamarin domin daukar matakin da ya dace.

Da yake karin haske, Kakakin Rundunar, DSP Suleiman Yahya Nguroje, ya ce, “Duk wanda aka samu da hannu a ciki za a kama shi a kuma gurfanar da shi.

Rundunarmu ba za ta lamunci duk wani taro da zai iya haddasa fitina a cikin al’umma ba.

“Kwamishinan ’Yan Sanda ya ba da umarnin a yi bincike domin gano wadanda suka shirya dabdalar da kuma wurin da aka shirya gudanar da shi, domin Rundunar ba za ta amince da duk wani nau’i na badala da zai harzuka jama’a ba,” inji shi.