✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon tsiraici a TikTok: Me ke damun ’Yan Arewa?

’Yan Arewa musamma mace, ballantana a ce a Kano, an san su da kamun kai da kaffa-kaffa.

A ’yan makonnin nan bidiyon tsiraicin wasu jaruman TikTok mata ’yan Arewacin sun yamutsa hazo.

Dambarwar bidiyon ’yan TikTok din daga Jihar Kano ya sa yawancin masu tsokaci kan wannan lamari nuna damuwa da diga aya kan dalilan yin irin wannan abin assha da kuma yaduwarsu.

A makon jiya aka yi fama da dambar bidiyon tsiraicin Hafsat Baby, wanda ya tayar da kura.

Dambarwar Babiana

Bidiyon tsiraicin ’yar TikTok da ya fara fito tayar da kura a ’yan makonnin nan shi ne na Babiana, wadda aka fi sani da Queen of Update, inda bidiyon ya fito bayan ’yan makonni da mutuwar aurenta.

Wannan ya sa ake ganin wuce gona da irin da ’yan TikTok mata daga Arewa suke yi akwai alamar kidahumanci da sunan neman mabiya ko kuma daurin gindi da kuma uwa-uba, rashin tunanin ranar gobe.

A hirar da aka yi da ita kan dambarwar, Babiana ta yi ikirarin cewa, wasu ne suka yi mata barazana domin ta ba su makudan kudade ko su saki bidiyon nata duniya ta gani, ita kuma ta ce shege ka fasa, shi ne suka yada bidiyon.

Tambayar da amsarta ta kasa samuwa ita ce, wa ya dauki bidiyon, mene ne dalili, sannan ya aka yi ya shiga hannunsu?

Hafsat Baby ta yamutsa hazo

Ana cikin wannan cakwakiya kuma, a makon jiya kafofin sada zumunta suka sake daukar zafi bayan fitar da bidiyon wata ’yar TikTok a Kano, Hafsat Baby.

A safiyar Litinin da ake hutun Ranar Takutaha a jihar ce Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya wallafa bidiyon wasu mata da hukumar ta cika hannu da su, ciki har da Hafsat Baby.

Amma daga bisani malamin ya cire bidiyon, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Aminiya ta nemi jin dalili, inda Babban Daraktan hukumar, Abba Sa’id Sufi ya shaida mata cewa, hukumar ta gano cewa wadda aka kaman ba Hafsa ba ce, sai dai suna kama, har a yanayin jikinsu.

Sai dai ya ce, suna hakon Hafsa domin ganin ta girbi abin da ta shuka.

Ina Dalili?

Ita kuma a nata ƙaulin, a cikin wani sakon sauti a Tiktok, Hafsat Baby ta bayyana cewa, tsohon bidiyo ne da aka yi sama da shekaru biyu da suka wuce.

Ta ce wai, ta fito ne kawai daga wanka sai ta ɗauki kanta a Snapchat, amma ba ta ajiye a wayarta ba, kuma ba wani ta tura wa ba.

Don haka, a cewarta, ba ta san yadda aka yi bidiyon ya fita duniya ba, domin ta riga ta goge shi daga wayarta kuma ba wanda ta taba tura wa. Shin hankali zai karbi wannan dalilin?

Ƙara lalacewar lamarin

Amma irin haka ta sha faruwa da masu amfani da kafofin sada zumunta.

Daga masu fitowa baro-baro suna batsa da sunan sayar da maganin hakkin maye, sai masu ikirarin nishadi, da masu ashariya da rashin kunya.

Iya-shegen ya kai ga har da masu harkar madido da luwadi da sauransu, kuma har yanzu sai sabon salo suke bullo da shi.

Shafaffu da mai

Ana ganin akasarinsu ko an kama su, ba hukunci mai tsauri ake yi musu da zai zama darasi ba, wasunsu kuma ana za ce shafaffu ne da mai, duba da dambarwar Murja Kunya, wadda bayan kotu ta ba da umarnin tsare ta a kurkuku, wasu masu ido da kwalli suka hada baki, aka fito da ita kuma babu abin da ya faru.

Wani abin mamaki shi ne ko da sun shiga hannun hukuma, hankulan masu fada-a-ji ke tashi.

Ɗan saukinta shi ne lokacin da irin wadannan matasa ke fitowa su ce, sun tuba, amma kafin a je ko’ina sun ta da tuban.

Ko waɗannan da aka ambata, cikinsu babu wadda ba ta taɓa irin haka ba, ashe tuban muzuru ne.

A game da wannan tataburza da zargin wasu masu amfani da soshiyal midiyana Arewa da amfani da kafofin wajen yin iya-shege domin tara mabiya, kama daga shigar banza da manganun batsa da dangoginsu na nuna rashin tarbiyya.

Duk da cewa kafofin sada zumunta sun zo da alheransu daga kuma akasin haka, amma ‘yan Arewa musamma mace, ballantana a ce a Kano, an san su da kamun kai da kaffa-kaffa wajen duk abin da zai zubar da mutuncinsu.

Ina amfanin da suka zama zakka a kafofin sada zumunta, alhali sun fito daga al’umma mai alfahari da addini da kamun kai?

Idan kuɗi ko mabiya ake nema, akwai ɗimbin waɗanda suka tara, ta shiga harkoki masu amfanar jama’a.