Ana zargin wani likita ɗan ƙasar Indiya da yin sanadiyar mutuwar wani yaro ɗan shekara 15, bayan tiyatar da ya yi masa a lokacin da yake kallon bidiyon yadda ake cire tsakuwa daga matsarmama (gallbladder) ta hanyar tiyata a YouTube.
Ajit Kumar Puri, likita ne a Asibitin Ganpati da ke Saran a Jihar Bihar ta Indiya, wanda ake tuhumar sa da yin silar mutuwar wani matashi a yankin ta hanyar yi masa tiyata ba tare da sanin sa ko ƙwarewar aiki ba.
Iyayan yaron sun yi iƙirarin cewa, sun kawo shi asibiti a makon da ya gabata bayan ya yi amai da yawa.
An kwantar da shi a asibitin kuma alamun ciwon ya ragu, amma Dakta Puri ya yanke shawarar cewa dole ne ya yi wa yaron tiyata don cire tsakuwa da ke haifar wa da yaron amai.
Bayan likitan ya aiki mahaifin matashin zuwa wani wuri, sai ya yi masa tiyata ba tare da amincewar iyayensa ba, lamarin da ya haifar da tsananin yanayin ciwon yaron.
Daga ƙarshe Dakta Puri ya yanke shawarar a ɗauke yaron zuwa wani asibiti, amma yaron ya mutu a hanya, inda ya rantaya a na kare, ya bar gawarsa a kan matattakalar asibitin Patna.
Irin wannan abin takaici yana faruwa lokaci zuwa lokaci, amma a wannan karon, ’yan uwan matashin sun ce Dakta Ajit Kumar Puri yana da dalili mai kyau na gudu, la’akari da yadda ya tafiyar da lamarin.
Sun yi iƙirarin cewa, ba shi da basirar yin aikin da a qarsthe ya yi silar mutuwar majinyacin, yayin da aka gan shi yana kallon yadda ake cire duwatsu daga matsarmama (gallbladder) a YouTube a lokacin da yake tiyatar.
“Mun kwantar da shi daga bisani kuma amai ya tsaya ba da jimawa ba. Amma likitan, wato Ajit Kumar Puri ya ce a yi masa tiyata.
“Ya gudanar da aikin ne ta hanyar kallon bidiyo a YouTube. Dana ya mutu daga baya,” in ji mahaifin yaron da ya shaida wa Kafar Labarai ta NDTV.
Bayan yaron ya farfaɗo daga tiyatar da aka yi masa, ya fara ƙorafin tsananin ciwo amma da Dakta Puri ya fuskanci iyayen marar lafiyan na ƙorafi, sai ya yi musu tsawa yana tambayarsu ko su likitoci ne?
Abin takaici, sai yanayin ciwon majinyacin ya ƙara tsananta, wanda a ƙarshe dole aka sake sauya wani shiri.
A wannan lokacin ne likitan ya yanke shawarar mayar da matashin zuwa wani asibiti, inda a kan hanyar zuwa ya ce ga garinku nan.
“Yaron yana cikin raɗaɗin jin zafi. Da muka tambayi likitan dalilin da ya sa yake jin zafi, sai ya fara yi mana fada, ya tambaye mu ko mu likitoci ne.
“Da yamma sai yaron ya daina numfashi. An farfaɗo da shi (tare da na’urar CPR) sannan aka garzaya da shi zuwa asibitin Patna, inda ya rasu a kan hanya.
“Sun bar gawar yaron a kan matattakalar asibitin sun gudu’’, in ji kakan matashin.
‘Yan sanda sun shigar da ƙarar Dakta Puri kuma hukumomi suna jiran sakamakon binciken gawar.
A halin da ake ciki, likitan da ya gudu ba a san inda ya nufa ba, inda dangin yaron da ’yan sanda ke zargin cewa likitan ba ƙwararre ba ne.
Samun likitocin bogi ba sabon abu ba ne a Indiya, domin ko a farkon wannan shekarar, an gano wani mutum yana aikin likitanci a Mumbai da digirin matarsa.