Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Unguwar Bompai ta Jihar Kano ta bayar da belin fitacciyar jarumar TikTok da aka kama kan zargin ɓata tarbiyya, Murja Ibrahim Kunya.
Kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Saminu ta sanya ƙa’idojin da za a cika kafin a bayar da belin Murna, daga ciki za a ba da kuɗi Naira dubu ɗari biyar.
Haka kuma kotun ta umarce ta da ta kawo mutanen da za su tsaya mata guda biyu.
Kotun ta ce dole ne ɗaya ya kasance dan uwanta na kusa, yayin da ɗayan kuma zai kasance wanda ya mallaki kasa mai daraja a Jihar Kano.
- Tagwayen farfesoshin da suka yi aure rana guda kuma suke karantarwa a jami’a daya
- An Ƙwaci Buhunan Shinkafa 29 A Hannun Kwastam A Kebbi
Idan ba a manta ba Hukumar HISBAH ce ta miƙa Murja ga kotu domin bincike da ɗaukar mataki muddin an sameta da laifin da ’yan unguwarsu suka kai kararta.
Kamun Murja Kunya ya janyo ce-ce-ku-ce wanda wasu ke ganin yana da nasaba da abin da ya janyo Kwamandan HISBAH Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi murabus ɗin kashin kai a kwanakin baya, kafin daga bisani a daidata shi da Gwamnatin Kano ya koma bakin aiki.