Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya isa ofishinsa a karon farko bayan ya dawo bakin aiki.
Karon farko ke nan da mashahurin malamin ya shiga harabar ofishin hukumar tun da ya sanar da murabus dinsa a ranar Juma’a kan sukar da Gwamna Abba Kabir ya yi wa salon kamen hukumar a aikinta na yaki da masu badala a jihar.
Murabus din malamin ya bar baya da kura inda yi ta ba shi baki, gwamnatin jihar kuma ta shiga bikon sa.
A karshe ranar Litinin da dare aka shawo kansa a wani taron sirri da Zauren Malaman Kano ya jagoranta a gidan gwamnatin jihar.
- Daurawa Ya Ba Batagari Wa’adin Mako 2 su tuba
- Kada Ku Kara Farashi A Ramadan —Sarkin Kano ga ’yan kasuwa
Aminiya ta ruwaito cewa dawowar Daurawa kan kujerarsa ke da wuya ya ba wa masu aikata badala a jihar da su tuba ko kuma su gamu da fushin hukumar.