✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun janye gayyatar da suka yi wa Sanusi II kan hawan sallah

Kakakin ya ce wasu manyan mutane ne suka shiga lamarin domin kaucewa ruɗani.

Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, kan hawan sallah.

Maimaikon Sarkin ya je Abuja domin yi masa tambayoyi, Sufeto Janar ya umarci rundunar ’yan sandan jihar ta je har fadarsa domin yi wa Sanusi II tambayoyi.

Kakakin ’yan sanda na ƙasa, Olumuyiwa Adejobi ne, ya bayyana hakan, inda ya ce an janye gayyatar ne bayan da wasu manyan mutane a ƙasar suka shiga lamarin.

Ya ƙara da cewa ’yan sanda na son kauce wa duk wani da zai danganta lamarin da siyasa ko wani abu daban.

Idan ba a manta ba hedikwatar ’yan sanda ta ƙasa ce, ta gayyaci Sarkin, domin ya bayar da bayani game da wani abin da ya faru a lokacin bikin Sallah a Kano.

Tun da farko, rundunar ’yan sandan jihar, ta dakatar da duk wasu hawan Sallah da suka haɗa da jerin gwanon dawakai, saboda matsalar tsaro.

Amma a ranar 30 ga watan Maris, yayin da Sarkin ke tafiya zuwa filin Idi na Ƙofar Mata domin Sallar Idi, an kashe wani jami’in sa-kai da ke tsaronsa ta hanyar caka masa wuƙa, sannan wasu kuma sun jikkata.

Bayan haka, wasu majiya sun ce Sufeto Janar na ’yan sanda, Kayode Egbetokun, ne, ya umarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya kama Sanusi II.

Sai dai Kwamishinan ya shaida masa cewa abin da ya faru bai shafi karya dokar hana hawan Sallah ba, kuma Sarkin bai hau doki ba wajen ziyarar gidan gwamnati kamar yadda ake yi a da.

Sai dai duk haka Sufeton ya umarci sashen leƙen asiri na ’yan sanda da su gayyaci Sarkin zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.