✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ragargaji ’yan bindiga sun ceto mutum 15 a Neja

Maharan sun tsere sun bar mutanen da suka sace bayan sun sha luguden wuta a hannun ’yan sanda.

Wasu ’yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannun ’yan sanda a yankin Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

’Yan sandan sun ragargaji ’yan bindigar, suka fatattake su ne bayan bata-tarin sun kai hari kauyen Jellako da ke karamar hukumar suka yi awon gaba da mutum 15.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, “A ci gaba da aikin sharar dajin da muke yi domin kawar da ’yan bindiga da sauran manyan laifuka, a ranar 9 ga Mayu, 2022, da misalin karfe 8.30 na dare, mun samo rahoton motsin ’yan bindiga da ake zargi a kusa da kauyen Jellako a Karamar Hukumar Rafi, nan take kuma ’yan sanda suka yi wa wurin dirar mikiya.

“Da ’yan bindigar suka tabbatar jami’anmu za su ci karfinsu, sai suka ranta a na kare zuwa cikin daji.

“A yayin da suke tserewa domin tsira da rayuwarsu, sun bar babura biyu da wasu mutum 15 da suka yi garkuwa da su daga wurare daban-daban.”

A cewar Abiodun, an kubutar da mutanen ba tare da sun samu wata matsala ba, aka kai su asabiti domin duba lafiyarsu, kafin nan gaba a mika su ga iyalansu.