✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun mamaye Majalisar Dokokin Kuros Riba

An baza jami'an tsaro da nufin ko ta kwana.

’Yan sandan sun mamaye dukkanin hanyoyin zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kuros Riba.

Tun da misalin karfe 6 ba safiyar Talata ’yan sandan suka mamaye harabar majalisar.

Kowace tawagar ’yan sandan na dauke da makamai suna jiran ko-ta-kwana a cikin harabar majalisar.

Wasu daga cikinsu kuma na tsaye a gaban ofishin gwamnan jihar, Ben Ayade.

Daga daya bangaren kuwa magoya bayan jam’iyya ne suka yi curko-curko, yayin da wasu daga cikin ’yan barandan siyasa ke ’yan zuke-zuke.

Masu ababen hawa kuwa sun samu tsaiko sakamakon dandazon jami’an tsaron da aka baza a kan hanyar, wanda hakan ya haifar da cunkuson ababen hawa a hanyar.

Wannan na zuwa ne bayan hukuncin da alkalin wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, Taiwo Taiwo, ya yanke kan tsige wasu ’yan majalisa 18 da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC a jihar.

Jam’iyyar APC mai mulki ta daukaka kara kan hukuncin kotun.