Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta karyata rahoton fashewar wani bam yau Laraba a unguwar Maitama da ke birnin Tarayya Abuja.
Mazauna birnin na Abuja sun yi ta kururuta cewa bam ne ya tashi cikin wasu sakonnin da suka rika tashe a dandalin sada zumunta na X.
Sai dai binciken da rundunar ta gudanar, ta gano cewa wata kwantenar karfe ta shara ce ta dauki zafi kana ta kama da wuta, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar wasu masu kwashe shara biyu, wadanda a halin yanzu suke asibitin Maitama suna samun kulawar likitoci.
A sanarwar da rundunar ‘yan sanda ta fitar da ke dauke da sa hannun mai magana da yawunta Josephine Adeh ta ce “tuni aka tura tawagar masu ba da agajin gaggawa da kuma sashen kawar da ababen fashewa don tantance lamarin.”
“Lamarin ya auku ne a ranar 24 ga watan Janairu da misalin karfe 11:45, kusa da wata bola a wajen harabar Ofishin Bureau of Public Enterprise da ke Maitama a Abuja ba bam ba ne,” a cewar sanarwar.
Rundunar ta bukaci al’umma su yi taka-tsan-tsan tare da kiyaye amfani da kwantenar shara ta karfe, a maimakon hakan ta ba da shawarar a rika amfani da roba don zuba shara, don rage hatsarin zafin da karfe ke dauka.