✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kwato shanu 293 daga barayin dabbobi

A ranar Juma’ar da ta wuce ne ’yan sandan  Jihar Kaduna suka kwato shanu 293 daga hannun wasu barayin shanu, bayan wani samame da suka…

A ranar Juma’ar da ta wuce ne ’yan sandan  Jihar Kaduna suka kwato shanu 293 daga hannun wasu barayin shanu, bayan wani samame da suka kai maboyar barayin shanun wanda ba a fadi sunan dajin ba.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Umar Shehu ne ya sanar da haka a lokacin da yake nuna wa manema labarai wasu ’yan fashi da makami da rundunar ta yi nasarar kamawa.
“Mun yi nasarar kwato shanu 293 a maboyar barayin shanu a cikin wani daji, bayan artabun da suka yi da jami’anmu sai suka gudu suka bar makamansu da kuma shanun. Haka rundunarmu ta yi nasarar kama wasu barayi uku wadanda suka dade suna addabar jama’a a unguwannin da ke Kudancin Kaduna. Har ila yau rundunarmu ta yi nasarar kama wasu ’yan fashi bakwai bayan sun shiga gidan wani mutum a Kinkinau, Tudun wadan Kaduna da jami’anmu suka samu labari sai suka yi wa gidan kawanya inda suka kama barayin su bakwai an kuma samu bindigogi da alburasai a hannunsu,” inji shi.
Kwamishinan ya ce akwai wasu ’yan fashi da suka mutu a artabun da suka yi da ’yan sanda a lokuta daban-daban a sassan jihar.
daya daga cikin wadanda ake zargi da yin fashi a Kudancin Kaduna mai suna Kingsley Ameachi da ake wa lakabi da Mopol ya shaida wa Aminiya cewa shi tsohon dan sanda ne kuma ya yi aiki ne a Jihar Kano kafin a sallame shi daga aiki a shekarar 2015.
A wani labarin Kwamishinan ’yan sandan Jihar Kaduna Umar Shehu ya ce rundunarsa ta kaddamar da wani shiri na yaki da mashaya da masu tu’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.
Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake tarbar shugaban cibiyar kula da masu tu’ammali da miyagun kwayoyi da koya musu sana’o’i (Niggas Rehabilitation Centre) da ke Rigasa Malam Lawal Maduru da aka fi sani da Malam Niga wanda ya kai masa ziyara a ofishinsa.
Kwamishinan ya ce sun sha alwashin kawar da tu’ammali da miyagun kwayoyi ne saboda duk wani laifi da matasa ke aikatawa kamar sata da sace mutane da fashi da makami sai sun sha kwaya suke aikatasu.
A cewar Kwamishinan rundunarsa ta gano wuraren da ake sayar da miyagun kwayoyi 48 a jihar.
Sai ya yaba wa Malam Niga saboda kokarin da ya yi na kafa cibiyarsa ta warkar da masu shaye-shaye.
Malam Lawal Maduru ya shaida wa Kwamishinan cewa a shirye suke wajen taimaka wa ’yan sanda domin cimma burinsu na kawo karshen masu sayar da kwayoyi a cikin jama’a.
Ya ce akwai matasa kusan dubu biyu a cibiyar wadanda suke karbar magani tare da koyon sana’o’i daban-daban.