✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun kwato shanu 275 daga ’yan bindigar Kaduna

’Yan sandan sun yi nasarar kwato shanu daga hannu ’yan bindiga a Jihar Kaduna. 

’Yan sandan sun yi nasarar kwato daruruwan shanu daga hannun ’yan bindiga a Jihar Kaduna.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Mohammed Jalige, ya ce jami’ansu da ke yin sintiri a yankin sun yi kwato shanu 137 daga hannun ’yan bindigar a yankin Zariya.

“A ranar 29 ga Afrilun 2021, jami’an ’yan sanda sun kwato shanu 137 cikin shanu 138 da ake nema, kuma tuni aka mayar wa da masu shanun dabbobinsu,” a cewarsa.

Ya ce, ranar 20 ga watan Afrilun kuma, Rundunar ta rahoto daga jami’inta mai kula da yankin Afaka kan yadda makiyaya ke gudanar da harkokinsu a yankin.

“An yi nasarar karbe shanu 138 daga hannun wasu ’yan bindiga inda aka kama su za su yi awon gaba da su.

“Ba mu yi kasa a gwiwa ba sai da muka tabbatar an karbe shanun.

Jalige ya ce, ’yan bindigar guda biyun da aka kama har yanzu ana gudanar da bincike a kansu.

“Muna iya bakin kokarinmu na tabbatar an kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su,” inji shi.