’Yan sandan sun yi nasarar kwato daruruwan shanu daga hannun ’yan bindiga a Jihar Kaduna.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Mohammed Jalige, ya ce jami’ansu da ke yin sintiri a yankin sun yi kwato shanu 137 daga hannun ’yan bindigar a yankin Zariya.
- Za a biya ’yan fansho karin kudi a watan Mayu
- COVID-19: NAFDAC ta amince da rigakafin Pfizer
- An kama barawon da ya sace wayar salula 273 a Katsina
“A ranar 29 ga Afrilun 2021, jami’an ’yan sanda sun kwato shanu 137 cikin shanu 138 da ake nema, kuma tuni aka mayar wa da masu shanun dabbobinsu,” a cewarsa.
Ya ce, ranar 20 ga watan Afrilun kuma, Rundunar ta rahoto daga jami’inta mai kula da yankin Afaka kan yadda makiyaya ke gudanar da harkokinsu a yankin.
“An yi nasarar karbe shanu 138 daga hannun wasu ’yan bindiga inda aka kama su za su yi awon gaba da su.
“Ba mu yi kasa a gwiwa ba sai da muka tabbatar an karbe shanun.
Jalige ya ce, ’yan bindigar guda biyun da aka kama har yanzu ana gudanar da bincike a kansu.
“Muna iya bakin kokarinmu na tabbatar an kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su,” inji shi.