Rundunar ’Yan Sanda Reshen Jihar Zamfara ta fatatttaki ’yan bindiga tare da kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi a Karamar Hukumar Shinkafi ta Zamfara.
Rundunar ta bayyana haka ne a ranar Asabar a birnin Gusau ta bakin kakakinta, SP Muhammad Shehu.
- An gurfanar da Matashi saboda cizon Budurwarsa a Mama
- ‘Na ga yadda ake horar da yara su zama ’yan bindiga’
- Wata mata ta antaya wa kishiyarta tafasasshen ruwa
- Yadda na haihu a hannun ’yan bindiga —Mai jego
Shehu ya ce, “ranar 2 ga Janairu, 2021 da misalin karfe 4:30 na asuba, rundunar ta samu rahoton cewa ’yan bindigar da yawa sun yi tsinke a garin na Shinkafi da niyyar yin garkuwar da mutane da ba su ji ba, ba su gani ba a yankin.
“Tawagar rundunar hadaka ta PMF/CTU da rundunar Operation Puff Adder suka dauki mataki cikin hanzari wurin kare farmakin na masu garkuwar.
“Har-ila-yau, mun kubutar da wani mutum mai suna Samaila Langa mai shekara 30, wanda barayin mutanen suka sace shi tare da hadin kan jami’an ’yan sanda da tubabbun masu garkuwar.
“Tuni muka sada shi da iyalansa bayan da lamura suka daidaita. Mun kuma samu karfin guiwar ci gaba da gudanar da sintiri a yankin na Shinkafi da kewaye”, inji Shehu.