’Yan sanda sun koka kan rashin biyan su kudaden da aka ware musu na abinci a yayin da suke aikin samar da tsaro a zaben gwamnan Jihar Anambra.
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa akalla jami’anta 5,000 ne ba a biya su kudaden alawus din da aka ware musu na aikin samar da tsaro a zaben na ranar Asabar ba.
- Yadda ’yan Arewa mazauna Anambra suka yi zaben gwamna
- Najeriya A Yau: Yadda aka shirya zaben Gwamnan Anambra
Wani dan sanda da aka tura wata rumfar zabe a gundunar Agabana 2 da ke Karamar Hukumar Njikoka ta jihar ya koka ga wakilinmu game da rashin ba su na abinci a zaben, wanda ake fatar samun sakamakonsa a ranar Lahadi, saboda matsalar na’urar tantace masu zabe a wasu wurare.
Akalla ’yan sanda 34,500 ne aka tura domin samar da tsaro a zaben da ke gudana a kananan hukumomin jihar 21 a ranar Asabar.
– Shugaban ’Yan Sanda ya sa a tura masa sunayensu
A kan haka ne Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya umarci kwamandojin rundunar da ke kula da zaben da su tura masa da jerin sunayen duk jami’an da ke aikin da ba biya su kudaden alawus dinsu ba.
Da yake bayani a Dakin Kula da yadda zaben ke gudana a Cibiyar Kula da Cigaban Dimokuradiyya (CDD), kakakin ’yan sandan Najeriya, Frank Mba, ya ambato Alkali ya alakanta matsalar rashin biyan kudaden da kurakuren da ke cikin jerin sunayen jami’an da aka tura.
“Mun gano cewa wasunsu ba su karbi kudadensu ba, sakamakon kurakuran da aka yi wajen bayar da bayanansu, ko kuma wata matsala a hanyar sadarwa,” inji shi.
Mba ya ce kawo yanzu 29,000 daga cikin ’yan sanda aka tura zaben gwamnan Anambran sun riga sun karbi alawus dinsu.
“Shugaban ’Yan Sanda ya umarci kwamandoji da sauran shugabannin da ke kula da zaben su tattara sunayen jami’an da ba su samu alawus sinsu su tura ba tare da kuskure ba.
“Karon farko ke nan da kuma taba biyan jami’anmu kudaden tun kafin a fara gudanar da zaben.
“Zuwa Juma’a da ranar mun tura jami’anmu kimanin 34,000, amma yau ban duba ba. Amma ina kyautata zaton karin wasu za su samu kudadensu.”