Rundunar ’yan sanda ta Operation Yaki ta hallaka ’yan bindiga hudu a kan hanyar Saminaka zuwa Jos a Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne bayan ’yan sandan sun hangi wasu da ake zargin ’yan bindiga ne a cikin wata mota kirar Sharon a kan hanyar zuwa Jos.
- Majalisar Kano ta dakatar da gina shaguna a jikin Asibitin Zana
- Mutum 600 sun mutu a hatsarin mota a titin Kano zuwa Kaduna cikin wata 6 — FRSC
Ya kara da cewa rundunar ’yan sandan ta yi dauki-ba-dadi da ’yan bindigar na tsawon minti 30 a cikin daji.
Bayan dauki-ba-dadi ne suka yi nasarar kashe hudu daga cikin ’yan bindigar, suka kwato bindiga kirar AK-47 guda uku da sauran makamai da kuma harsasai.
A cewarsa, tuni suka fara gudanar da bincike kan lamarin, don samun bayanai daga matar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Yekini A. Ayoku, ya jinjina wa ’yan sandan kan nasarar da suka samu a kan ’yan bindigar.