’Yan sanda sun kashe wasu mutum uku tare da cafke wasu biyu da ake zargin ’yan bindiga ne a Jihar Ebonyi.
Rundunar ’yan sandan jihar ta sanar a ranar Laraba cewa, ’yan sandan sun kwato bindiga kirar AK-47 guda biyu, bindiga kirar gida daya, harsashin AK-47 guda 50, da dai sauransu daga hannun wadanda ake zargin.
- Najeriya A Yau: Fadi-Tashin Gwamnoni Don Cin Zaben 2023
- ’Yan sanda sun kashe dan bindiga sun cafke wani a Katsina
Kakakin rundunar, SP Onome Onovwakpoyeya, ya sanar a Laraba a Abakaliki cewa, “A ranar 7 ga Maris, da misalim karfe 23:45 na dare DPO din hedikwatar Ivo ya samu kiran waya cewar ’yan bindiga sun kai hari, sun kone motoci biyu da wani gidan mai.
“Nan take ya aike da jami’ansa zuwa yankin da lamarin ya faru, inda suka yi artabu suka kashe uku daga cikin ’yan bindigar, wasu kuma sun gudu da raunukan harbi.”
Kwamishinan ’yan sandan jihar, ya gargadi masu dayar ta zaune tsaye cewar ba su da mafaka a jihar.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su rika taimaka wa jami’an tsaro da sahihin bayanai da za su kai ga dakile miyagun ayyuka a jihar.