Akalla ’yan bindiga biyu ne suka gamu da ajalinsu, yayin da wasu da dama suka tsere da raunuka bayan wata arangama da ‘yan sanda a Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, inda ‘yan sandan suka yi musayar wuta da ‘yan bindigar a gidan wani Sarkin Fulanin kauyen Danmarke, da ke gundumar Dagwarwa a Karamar Hukumar Kurfi ta jihar.
- Yin Sallar Tahajjud a gida ya fi lada —Sheikh Ibrahim Khalil
- Gwamnati za ta binne gawarwaki 49 a rami guda a Kaduna
Wata majiya ta ce ‘yan bindigar masu yawan gaske sun yi ta harbe-harbe da bindigogi kirar AK 47 a kauyen a lokacin da jami’an tsaro suka isa kauyen, bayan sun amsa kiran neman kawo dauki.
Bayanai sun ce mai magana da yawun ‘yan sandan reshen yankin Kurfi ne ya jagoranci artabun da aka yi da ‘yan bindigar kuma aka samu nasarar fatattakar su.
Bayan arangamar an gano gawar wasu ‘yan bindiga biyu, sannan kuma an kwato wasu shanu da suka sace.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Gambo Isah ya fitar, ya ce rundunar ta gano cewa wasu da dama daga cikin yan ta’addar sun tsere da raunin bindiga.
Kazalika, ya ce suna gudanar da kwarya-kwaryar bincike don gano inda wadanda suka samu rauni suka shiga.
CSP Isah a madadin rundunar ‘yan sandan ya yi kira ga al’ummar yankin da su kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su, idan suka samu labarin wanda ya samu rauni sakamakon harbin bindiga.