Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta yi nasarar harbe wasu ’yan bindiga biyu a kauyen Riheyi da ke gundumar Fatika a Karamar Hukumar Giwa ta jihar.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige ya fitar ranar Talata.
- Har tukin tasi na taba yi don tsira da mutuncina – Shugaban Kasar Rasha
- An harbe matafiya 2, an sace wasu da dama tsakanin Kaduna da Zariya
Ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Litinin, yayin da ’yan sandan kwantar da tarzoma suka kai sumame kan ’yan bindigar.
Ya ce lamarin ya kai ga musayar wuta tsakanin ’yan sanda da maharan, har aka hallaka mutum biyu daga cikinsu, tare da kwace bindigogi kirar AK47 guda biyu da kwanson harsasai guda 10 da kuma babur guda daya.
Jalige ya kara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Mudassiru Abdullahi, ya jinjina wa jami’an rundunar kan kokarin dakile ’yan bindiga da suka yi.
Har wa yau, Kwamishinan ya umarci ’yan sandan jihar da su ci gaba da dagewa wajen bankado maboyar bata-gari da ke fadin jihar.
Sannan ya ce, sakamakon karatowar lokacin bukukuwan karshen shekara, yana da kyau jama’a su sanya ido sosai tare sa taimaka wa jami’an tsaro wajen samun nasara a ayyukansu.