’Yan sanda sun harbe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne har lahira a yankin Sankera na Jihar Binuwe.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Catherine Anene, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce ’yan sanda sun kuma ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a yayin da suke ƙoƙarin kama garkuwa da mutanen.
- ‘Yan ɗarikar Tijjaniya sun yi wa Sarki Sanusi II mubaya’a
- ASUU ta shiga yajin aiki a jami’o’i biyu a Kano
Anene ta bayyana cewa rundunar ta samu wannan nasara ne bayan da ta ƙara ƙaimi a faɗin jihar musamman a yankin Sankara.
Ta ce, “Wannan yunƙuri an yi shi ne domin mayar da manoman gonakinsu da kuma daƙile ’yan bindiga a yankin.
“A ranar 29 ga Mayu 2024 da misalin ƙarfe 0600, jami’an ‘Operation Zenda JTF’ sun kai farmaki maɓoyar masu garkuwa da mutane.
“Da ganin ’yan sandan, masu garkuwa da mutane ƙarƙashin jagorancin shugabansu, Tersue Dada, wanda aka fi sani da “Causer”, suka bude wa tawagar wuta, amma ƙarfin wutan ’yan sandan ya ci ƙarfinsu.
“Saboda haka, mutane uku da ake zargin sun samu raunukan harbin bindiga kuma daga ƙarshe an tabbatar da mutuwarsu a asibiti yayin da aka kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin; mai suna Terɓer Taɓershima daga yankin Tinenune, a Ƙaramar Hukumar Ukum.”
Kakakin ’yan sandan ta lissafa kayayyakin da aka ƙwato da suka haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, bindiga ƙirar gida, wayoyi, kakin jami’an tsaro da kuma babur.