✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kashe kwararren mai garkuwa da mutane

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kashe wani kasurgumin mai garkuwa da mutane wanda ya kware wajen yin garkuwa da mutane bayan ya karbi…

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kashe wani kasurgumin mai garkuwa da mutane wanda ya kware wajen yin garkuwa da mutane bayan ya karbi kudin fansa ya kuma kashe mutum.

Mutumin mai suna Mufutawu wanda aka fi sani da Pencil ya gamu da ajalinsa ne biyo bayan barun wutar da jami’an ‘yan sanda suka yi da shi a daren jiya. Dan garkuwa da mutanen shi ne ya jagoranci yin garkuwa da wasu ‘yan kasuwar canji biyu a Legas a watannin baya inda ya kashe su bayan ya karbi kudin fansa.

Rundunar ‘yan sandan ta dade tana nemansa ruwa a jallo tun bayan da ta kame abokan ta’asar sa uku.