’Yan Sandan Jihar Sakkwato sun kashe karamin Hakimin Gidan Bunu, Alhaji Adduwa da dansa Aliyu Abdullahi, yayin da suke tsare da mutum 13 cikinsu har da mace da ake zargi suna satar shanu da yin garkuwa da mutane a yankunan Karamar Hukumar Rabah da kewaye.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Sakkwato, Cordelia Nwewe ta bayyana wa taron manema Labarai da hukumar ta kira, cewa “Wadannan mutane da kuke gani a gabanku jami’anmu ne suka kama su kan zargin da ake yi musu na satar shanu da garkuwa da mutane. Gawarwakin nan biyu kuwa daya mai suna Aliyu Abdullahi an kama shi a kauyen Gawon Fulani a Rabah yana tuka babur kirar Kasiya dauke da bindiga AK47 da harsasai 30 a cikinta da kuma wata bindiga a gefensa. Jami’anmu da ke aiki a wurin suka kama shi, amma sai ya yi kokarin gudu, suka harbe shi aka kai shi asibiti ya rasu can.”
“Gawar ta biyu kuma Hakimin Kauyen Gidan Bunu ne, wanda shi ne jagoran wannan gungun kamar yadda Abdullahi ya sanar da ’yan sandan, abin da ya jagorance su ga tafiya gidansa, shi ma bayan sun tafi turjiyarsa da kokarin ya gudu ya sanya aka harbe shi, yana karbar magani a asibiti shi ma ya rasu,” inji ta.
Ta ce macen cikinsu ita ce mai ajiye musu bindigogi da ake kira Rahmatu Muhammad, ta amince tana da alaka da Dankani, mai kawo kaya ga gungun barayin. Sai kuma Madugu Alhaji Haruna wanda yake kula da zirga-zirgarsu da karbo kayan aiki ya mika su ga marigayi Alhaji Adduwa.
“Lauwali Aliyu shi ko a Karamar Hukumar Illela aka kama shi a kauyen Araba kan iyaka da Nijar dauke bindiga AK47 da harsasai a yunkurinsa na yin fasa-kwaurinsu don rabawa a Sakkwato da Kebbi da Zamfara. Kuma ya dade yana wannan kasuwanci da wani Ibrahim Galmi a Nijar. Ya tabbatar mana an yi fashi da makami da garkuwa da mutane tare da shi. Makaman yana karbarsu ne daga wani da ake kira Muhammad Dankani wanda aka fi sani da Amerika a kauyen Dingim, idan ya zo yakan bai wa Malama Ramatu Muhammad a kauyen Tursa a Rabah,” inji Cordelia.
Ta ce sun samu harsasai dubu hudu da bindigogi da dabbobi 900 da rakuma da barguna a wurin wadanda ake zargin.
Rahamatu Muhammad ta shaida wa Aminiya cewa kazafi ake yi mata “Allah Ya sani ku dube ni ku gani in na yi kama da wadda za ta aikata irin wannan, sharri ne aka yi mini. Ali ya ce wai ina ajiye da bindigogi Danrani ya ba ni su, sharri ne kuma ya yi min haka ne don yana tare da dan uwanmu, a tare suke sayar da bindigogi, fadan da nake yi musu su daina ne suka sanya ni ciki,” inji ta
Madugu Alhaji Haruna kuwa cewa ya yi ya karbo bindigogi sau hudu, na farko an ba shi Naira dubu 80, na biyu 100, na uku 200, na hudu 300. Kuma ya ce an taba zuwa da shi kauyen Kware aka yi aiki aka ba shi Naira dubu 400, sannan an yi da shi a kauyen Kasarawa, amma shi ba a taba kashe mutum tare da shi ba, kwadayi ne kawai ya ja shi shiga wannan harka duk da ya san hadarinta.
Shugaban ’Yan Banga na Karamar Hukumar Rabah, Yusuf Muhammad ya ce tare suke aiki da ’yan sanda a yankin don su ga lallai sun tarwatsa batagari a yankin, suna shiga daji sosai kuma suna samun nasara don su ne silar samun wannan nasara da aka yi ta kama wadannan barayi.
Ya ce suna bukatar gwamnati ta tallafa musu da abubuwan hawa da sanya ’yan sanda su rika bin su a lokacin da za su fita aikin shiga daji, don in sun fatattaki barayin suka gudu ’yan sanda su rike.