✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Boko Haram sun kashe mutum 12 a Borno

Cikin wadanda aka kashe akwai ’yan sa-kai biyu da wasu mutum 10 da suka fita debo itacen girki.

Mayakan Boko Haram sun halaka mutum goma sha biyu da jikkata karin biyu bayan wani hari da suka kai kan kauyen Bokko Ghide a Karamar Hukumar Goza ta Jihar Borno.

Wakilinmu ya ruwaito cewa cikin wadanda aka kashe akwai ’yan sa-kai biyu da wasu mutum 10 da suka fita debo itacen girki.

Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mayakan sun yi wa ’yan sa-kan kwanton bauna a kan hanyar Kirawa da ke gudunmar Pulka.

“Sun fita neman itace ne a jeji a ranar Asabar, yayin da yaran [mayakan Boko Haram] suka yi musu kwanton bauna, inda suka kashe mutum 10 sannan wasu suka ji munanan raunuka.

“Mun binne mutum 10 sannan biyu da suka jikkata an mika su asibiti.

“Abin takaici shi ne ’yan sa-kai biyu sun sadaukar da rayuwarsu wajen kare mutanenmu wadanda aka kashe ranar Juma’a.”

Bayanai sun ce harin ya auku ne yayin da ake kokarin ganin an mayar da jama’ar yankin garuruwansu don su ci gaba da rayuwa, bayan kwashe shekaru da dama suna gudun hijira a wasu wurare saboda hare-haren na ’yan Boko Haram.