‘Yan sanda sun bindige wasu mutum bakwai da ake zargi ‘yan fashi ne a wata musayar wuta a jihar Binuwai.
Harbe-harben an yi shi ne a kan titin da ya tashi daga Makurdi babban birnin jihar zuwa Lafiya a jihar Nasarwa.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Binuwai Catherine Anene ta ce lamarin ya faru bayan’yan fashi sun kai wa shingen bincike na ‘yan sanda hari suka kashe wani sufeta suka dauke bindigar ‘yan sanda a rana 4 ga watan Yunin da muke ciki.
Ta ce sakamakon hakan ne a Rundunar ta tura jami’anta a kan titin domin bin sahun wadanda suka yi aika-aikar.
Jami’ar ta ce ‘yan sandan da aka tura sun je sun iske ‘yan fashin sanye da kayan ‘yan sanda da sojoji a kan titin.
Daga nan sai suka bude wa ‘yan sandan wuta lamarin da ya yi sanadiyyar musayar wuta da a ciki bakwai daga cikin ‘yan fashin suka samu raunukan da suka zama ajalinsu bayan an kai su asibiti.
Abubuwan da aka kwato daga ‘yan fashin sun hada bindigogin AK47 guda biyu da wasu kananan bindigogi da harsasai da adduna da sauransu.