✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun karyata labarin kashe mutum 10 a kusa da rijiyar mai a Bauchi

’Yan sandan sun ce labarin sam ba gaskiya ba ne

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta karyata labarin da ke yawo cewa wasu ’yan bindiga sun kai hari kan wasu yankunan da ke kusa da inda aka gano sabuwar rijiyar man fetur ta Kolmani, har suka kashe mutum 10.

Rahotanni dai a karshen mako sun yi ta yawo cewa wasu ’yan bindiga a kan babura sun kai hari wasu yankunan Karamar Hukumar Alkaleri cikin makon nan, inda suka halaka mutanen.

Sai dai ’yan sanda, ta bakin Kakakinsu a Jihar ta Bauchi, Ahmed Wakil, sun bayyana labarin a matsayin na kanzon kurege, wanda ko kadan babu kamshin gaskiya a cikinsa.

A cikin wata sanarwa da maraicen Lahadi, rundunar ta ce, “Kodayake ba mu san mummunar niyyar masu yada wannan labarin ba, amma hakan na iya yin zagon kasa ga yunkurin rundunar na yaki da bata-gari a fadin jihar.

“Saboda haka, muna so mu bayyana cewa labarin da ake ta yadawa ba gaskiya ba ne, kuma ya saba da abin da yake a zahiri.

“Ko kafin a kaddamar da aikin fara hakar man fetur a rijiyar Kolmani, rundunarmu ta samar da kayayyaki da yanayin tsaro mai inganci, kuma ta dada kaimi wajen tattara bayanan sirri kuma tana gudanar da sintiri don tabbatar da zaman lafiya,” inji sanarwar.

Kakakin ya kuma ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Aminu Alhassan ya shawarci kafafen yada labarai da su tabbatar suna tantance sahihancin labari kafin su yada shi, don kaucewa tayar da zaune tsaye.