✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama ’yan kungiyar BBOG

’Yan sanda sun kama membobin kungiyar BringBackOurGirls jiya biyo bayan tattakin da suka yi zuwa fadar shugaban kasa wanda suka yi wa lakabin:“#TattakinKungiyarBringBackOurGirlsZuwaFadarShugabanKasa”.   A…

’Yan sanda sun kama membobin kungiyar BringBackOurGirls jiya biyo bayan tattakin da suka yi zuwa fadar shugaban kasa wanda suka yi wa lakabin:“#TattakinKungiyarBringBackOurGirlsZuwaFadarShugabanKasa”.
 
A sakon kafar sadarwa ta tiwita da jagorar kungiyar, Oby Ezekwesili ta yada ta bayyana cewa an kama ta kuma an tsare ta tare da ’yan sauran membobin kungiyar.
 
“’Yan sanda sun kama ni tare da sauran membobin kungiyar BBOG a yanzu an tsare mu ba tare da wani laifi ba. Ana tsare da mu a ofishin rundunar ’yan sanda na Abuja. Amma ’yan sanda sun ki gaya mana dalilin da ya sa suke tsare da mu”. Inji ta.