Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu mutum biyar da ake zargi da aikata damfara a Ƙaramar Hukumar Tarmuwa.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar, ya bayyana cewa waɗanda aka kama sun haɗa da Abdullahi Suleman, Sani Salisu, da Nasiru Mohd, duk daga Jihar Gombe.
- Nan ba da jimawa za a ƙara kuɗin kiran waya da data — Gwamnati
- ’Yan bindiga sun sake sace mutum 46 a Zamfara
Sauran sun haɗa da Alhasan Illiya daga Potiskum, a Jihar Yobe; da Weti Mohd daga Ngorore, a Jihar Adamawa.
Rundunar haɗin gwiwa ta hukumar leƙen asiri ta SID ce, ta cafke su a Tarmuwa.
SP Dungus ya ce, “Waɗannan mutane suna amfani da dabaru irin na yaudara, suna tunkarar jama’a kamar matafiya da ke neman taimako.
“Bayan sun samu amincewa, sai su raba su da kuɗinsu da sunan taimaka musu wajen samun kuɗi cikin sauƙi.”
Ya ƙara da cewa, “A baya-bayan nan, sun damfari wani Mallam Audu Shehu daga ƙauyen Shekau na Ƙaramar Hukumar Tarmuwa Naira 500,000. Sai dai an samu kuɗin a lokacin bincike.”
Waɗanda ake zargin sun amsa cewa wannan ita ce damfararsu ta farko a Jihar Yobe, duk da cewa sun shafe sama da shekaru uku suna yin irin wannan damfara a Jihohin Adamawa, Gombe, da Taraba.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Garba Ahmed, ya jaddada ƙudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya yi kira ga al’umma da su yi taka-tsan-tsan da mutanen da ke nuna su matafiya ne ko jami’an tsaro amma suna shirin damfara.
Rundunar ta kuma shawarci mazauna jihar da su riƙa kai rahoton duk wani abu da su yarda ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da su don rage ayyukan ɓata-gari.