Rundunar ‘yan sanda a Jihar Jigawa ta yi nasarar cafke wasu mutum biyar da ake zargin ‘yan bindiga ne da kuma aikata fashi da makami a Karamar Hukumar Ringim ta jihar.
Kakakin ‘yan sandan Jihar, ASP Lawan Shiisu ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da Kamfanin Dillacin Labarai (NAN) ranar Litinin a Dutse, babban birnin Jihar.
- Ramadan: Wadanne kasashe ne suka fi kowanne dadewa kafin su sha ruwa da azumi?
- ‘Dakatar da Sheikh Nuru Khalid ba zai hana mu fadin gaskiya ba’
“Wadanda ake zargin na da hannu a aikata fashi da makami da kuma garkuwa da mutane tsakanin jihohin Jigawa da Kano.”
Shiisu ya ce wanda ake zargin da farko sun nuna sha’awar mika wuya ga jami’an tsaro.
Ya kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun yi samame tare da kame wani mai shekara 30 a Karamar Hukumar Ajingi da ke Jihar Kano.
Ragowar kuma sun shiga hannun ne a garuruwa daban-daban tsakanin Kano da Jigawa tun a ranar 26 ga wata Maris.
Ya ce a halin yanzu ababen zargin na ba da hadin kai wajen binciken da ake gudanarwa.
Shiisu ya ce za a mika su zuwa kotu da zarar an kammala bincike a kansu.