Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum, mai shekaru 35 daga ƙauyen Kunji da ke Kwadon, bisa zargin mallakar jabun kuɗi.
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama Kawu ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2025, a ofishin ’yan sanda na Lawanti, sannan aka kai shi ofishin Amada domin ci gaba da bincike.
- Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba
- Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba
Ya ce an samu dalar Amurka 1,000 da ake zargin na bogi ne (kimanin Naira miliyan 1.5), da kuma Naira 10,000 a cikin kayansa.
A yayin bincike, Kawu ya amsa cewa kuɗin na wani mutum ne.
’Yan sanda sun ce suna ci gaba da bincike domin gano wanda ya ba shi kuɗin.
Rundunar ta kuma ce za ta ci gaba da yaƙar masu ta’ammali da jabun kuɗi tare da tabbatar da cewa za ta sanar da jama’a yadda binciken ke tafiya.