’Yan sanda sun cafke kwamandan kungiyar IPOB da ake zargi da kashe Ahmed Gulak, tsohon hadimin shugaban kasa a bangaren siyasa na zamanin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Kakakin ’yan sandan Jihar Imo, CSP Michael Abattam, ya ce Las Kofur Nwangwu Chiwendu, wanda dubun tasa ta cika ya gudu ne daga aikin soja ya shiga kungiyar ’yan ta’addan.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Tabbatar Da Zaman Lafiya A Harkokin Zabe
- Majalisa ta bukaci CBN ya tsawaita wa’adin daina karbar tsohon kudi
“Da tawagarmu ta tare motar Gulak muka harbe shi, harsashi bai ratsa jikinsa ba.
“Da kaina na sauko daga mota na cire zoben da ke hannunsa sannan na harbe shi, nan take ya fadi a kasa matacce,” in ji gudajjen sojan.
A lokacin da aka yi holen sa a hedikwatar ’yan da ke Owerri a ranar Laraba, ya shaida wa ’yan jarida cewa ya shiga aikin soja a 2013, amma bayan ya samu kwarewa a fannin sarrafawa da gyaran manyan makamai, sai ya tsere a 2021 ya shiga kungiyar IPOB.
“Ya zama Kwamanda a reshen soji na IPOB (ESN) inda ya horas da ’yan kungiyar sama 1,000 kan sarrafa makamai da kai hare-haren ta’addanci.
“Ya amsa laifin kai hare-hare kan ofishoshin ’yan sanda da gine-ginen gwamnati a jihar nan,” in ji kakakin ’yan sandan.
Ya ci gaba da cewa gudajjen sojan mai shekara 34, wanda aka dade ana nema ruwa-a-jallo, kan sa yaransa su yi masa leken asiri kafin ya kai harin sari-ka-noke, sannan ya tsere zuwa wasu jihohi kafin dubunsa ta cika.
Kakakin ’yan sandan jihar ya ce Nwagwu ya amsa laifin jagorantar hare-hare da IPOB ta kai wa ofisoshin INEC a Jihar Imo, da ofisoshin ’yan sanda da garkuwa da mutane da fashi da kuma yi wa ’yan siyasa da jami’an gwamnati kisan gilla.
A cewar kakakin, an cafke Las Kofur Nwagwu ne a ranar 25 ga watan Disamba a garinsu, Amaohuru Nguru, da ke Karamar Hukumar Aboh Mbaise ta jihar.
Bayan shigarsa hannu, an kwato bindigogi da harsasai a wajensa.
Ya ce rundunar na ci gaba da gudanar da bincike inda suke samun bayanai daga wajensa don kama wadanda suke aiki tare da shi.