Rundunar ’Yan Sandar Jihar Kaduna ta tabbatar da kama wata mahaifiya da danta bisa zargin hada baki da kashe kanin mijinta saboda kudin toshin da aka ba ’yarta.
Kakakin rundunar a Jihar, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da kama matar mai suna Maimuna, wacce aka fi sani da Munari, tare da danta Abubakar Yahaya Gwamna mai shekaru 23 da haihuwa, a zantawarsa da Aminiya ta wayar salula.
- ‘Kusan sau miliyan 13 aka yi yunkurin yi wa Najeriya kutse yayin zaben Shugaban Kasa’
- Kamfanin Meta mallakin Facebook ya sake korar ma’aikata 10,000
Jalige ya ce ’yan sanda na ci gaba da tsarewa tare da binciken lamarin kuma ya ce da zarar sun kammala bincikensu za su gurfanar da su a gaban kotu.
Ana zargin Munari da sanya danta Abubakar Yahaya Gwamna, da ya kashe Babbansa, kuma kanin maigidanta mai suna Abdullahi Adamu Biso mai shekaru 26 da haihuwa mai sana’ar sai da kuli-kuli.
Ya ce a ranar Litinin da ta gabata ce Munari ta umarci danta da ta haifa, ya kashe kawunsa, kuma kanin mijinta Adullahi Adamu Biso, a kan sabanin kudin toshi da ya shiga tsakaninsu.
Marigayin ya cim ma ajalinsa ne ta hanyar sossoka masa wuka da dan yayansa ya yi masa sanadiyar sabani da ya shiga tsakaninsa da mahaifiyarsa.
Lamarin ya faru ne a Anguwar Zangon Shanu, Samaru da ke Karamar Hukumar Sabon Garin Zariyan Jihar Kaduna.
Bayanai daga al’ummar anguwar na cewa dukkansu ’yan uwan juna ne, kuma ’yan gida daya, domin auren zumunci aka kulla tsakanin mahaifin yaron da mahaifiyarsa.
Yayan marigayin mai suna Ibrahim Adamu Biso, ya shaida wa Aminiya cewa, “Rashin jituwar ya samo asali ne a kan kin yarda da ita matar yayan marigayin, Maimuna ta yi na kin yarda da cika alkawarin da aka yi wa abokin marigayin, Sabi’u Yusuf Mijinyawa na cewa za su aura masa ’yarsu wadda shi marigayi Abdullahi ne ya yi wa abokin nashi hanyar neman auran ’yar yayan namu inda ita kuma Maimuna daga baya ta ki amincewa.
“Don haka sai shi marigayin ya ce tun da haka ta faru to sai a mayar wa abokin nasa da duk irin abubuwan da aka san ya bai wa budurwar mai suna Tanzila Yahaya tun da baza a ba shi aurenta ba.
Wannan shi ne ya haifar da rashin jituwa tsakaninsu har da bakaken maganganu, bayan an shiga tsakani, sai ita Maimuna ta ce wa marigayi wallahi ita ba za ta yarda ba, kuma ya san halin ’ya’yanta don haka zata sa su daukar mata fansa.”
Ibrahim Biso yayan marigayin ya kara da cewa, “Ko minti 20 ba a yi ba da shi marigayi ya dawo shago wajan sana’arsa, sai ga daya daga cikinsu Abubakar Gwamna dauke da sharbebiyar wuka a hannu ya fada shagon marigayin, kafin a farga ya sossoka mishi wukar nan ta wuyansa da sauraran bangarorin jikinsa.
“Da jin ihu sai nan da nan muka kutsa shagon tun da dama wurin muke kasuwancinmu gaba dayanmu, muka ga abin da ya faru, to sai muka yi kokarin kama shi Gwamna muka kwace wukar, sannan muka dauki marigayin zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, inda a nan ne Allah ya karbi rayuwarsa sakamakon raunukan sukar wukar da Gwamna ya yi masa.
Ibrahim Biso ya kara da cewa sai dai ita Maimuna ganin irin barnar da shi dan nata ya yi, da kuma yadda al’ummar anguwar suka taso sai ta gudu, kuma har yau ba a san inda take ba.
Sai dai ya ce shi Gwamna wadda shi ne ya aikata kisan yana can hannun ’yan sanda a Kaduna, bayan kama shi da al’ummar anguwar suka yi suka mika wa ’yan sandan yankin Samaru.