’Yan sanda sun kama mutum biyu a wani samame da suka kai gidan iyalan attajirin nan mai suna Gupta a Afirka ta Kudu a wani bincike da gwamnati ke yi.
Attajiri Gupta dai wani haifaffun kasar Indiya ne da ke fuskantar tuhuma da zargin “makare hukumar kasar” ta hanyar amfani da dangantakarsa da Shugaba Jacob Zuma domin samun manyan kwangiloli daga gwamnati kamar yadda BBC ya ruwaito.
Tuni dai iyalan Guptan da Mista Zuma suka musanta wadannan tuhume-tuhumen da ake yi musu.
Ana tunanin alakar Shugaba Zuma da iyalan Gupta na cikin dalilin tursasa masa ya sauka daga mulki