’Yan sanda a Babban Birnin Tarayya Abuja sun kama mutum 14 da suka ce an sace musu mazakuta.
A cewar ’yan sandan, zargin da mutanen suka yi ya sa wasu fusatattun mutane sun dauki doka a hannunsu ta hanyar hukunta wadanda aka shafa wa kashin kajin a daidai lokacin da matsalar take dada karuwa a birnin.
- Kotu ta yanke wa wanda ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a coci ɗaurin rai da rai
- Tinubu ya nada wanda zai maye gurbin El-Rufa’i a matsayin minista daga Kaduna
Kwamishinan ’yan sanda mai kula da yankin babban birnin, Haruna Garba, ne ya bayyana hakan a hedkwatar ’yan sandan da ke Abuja, yayin da yake jawabi ga ’yan jarida ranar Talata.
Ya ce an kama mutanen ne saboda sun ba jama’a da ’yan sanda bayanan karya, yana mai cewa aikinsu ne kare rayuka da dukiyoyin mutane.
Haruna ya kuma ce, “Mutum sha hudun da suka yi da’awar an sace musu mazakutar mun kai su asibiti, inda likitoci suka tabbatar da cewa babu abin da ya samu mazakutar tasu, kuma tana aiki.
“A kan haka ne muka gurfanar da su a gaban kotu saboda yada bayanan karya da kuma tayar da hankalin jama’a.
“Ina kuma shawartar mazauna Abuja da su ja kunnen ’ya’yansu da su guji yada irin wadannan karairayin sannan su guji daukar doka a hannunsu,” in ji Kwamishinan ’Yan Sandan.