✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tinubu ya nada wanda zai maye gurbin El-Rufa’i a matsayin minista daga Kaduna

Tinubu ya bukaci Majalisar ta amince da nadin cikin gaggawa

Shugaban Koda Bola Tinubu, ya aike wa Majalisar Dattawa sunan Balarabe Abbas Lawal a matsayin minista daga Jihar Kaduna.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata wasika da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya karanta a yayin zamanta na ranar Talata.

Tinubu ya kuma bukaci majalisar ta amince da nadin Dr Jamila Bio Ibrahim da Ayodele Olawande su ma a matsayin ministoci.

An dai nada Balarabe ne domin ya maye gurbin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda a baya majalisa ta ki amincewa da nadin shi tare da Sanata Abubakar Sani Danladi daga jihar Taraba da kuma Stella Okotete daga jihar Delta) saboda dalilai na tsaro.

Sai dai Tinubu ya bukaci majalisar ta amince da sabbin nade-naden da gaggawa.

Balarabe dai ya taba zama tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna, kuma shugaban kwamitin karbar mulki na Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani a 2023.

%d bloggers like this: