✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama mota makare da bama-bamai a Kano

Hakan na zuwa ne kasa da mako daya bayan fashewar wani abu a unguwar Sabon Gari

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wata mota makare da na’urorin hada bama-bamai da bindigogi kirar AK-47 guda biyu a Jihar Kano.

Cikin sanarwa da mai magana da yawun rundunar a Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Lahadi, ya ce an samu nasarar wannan kamu ne biyo bayan rahoton sirri da suka samu a kan motar.

“A ranar 19/05/2022 muka samu wasu bayanan sirri cewa akwai wata mota kirar Mercedes Benz mai launin toka da ake zargin ta dauko na’urorin hada abubuwan fashewa da bama-bamai.

“Bayanan da muka samu sun nuna cewa motar ta taho ne daga Jihar Jigawa zuwa Jihar Kano.

“Wannan ce ta sanya Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi, nan take ya ta da wata tawagar kwararrun jami’ai da suka hada da masu warware duk wani nau’i na bama-bamai da kuma rundunar Operation Kan Ka Ce Kwabo.

“Da misalin karfe 4:30 na Yammacin wannan rana [Lahadi] ce wadanda ake zargin suka yasar da motar a rukunin gidaje na Bubbugaje da ke Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.

“Wani bincike na fasaha da rundunar ta gudanar ya nuna cewa motar makare take da na’urori da kayayyakin hada abubuwan fashewar.

“An kuma samu bindigogi kirar AK-47 guda biyu, kwanson alburusai guda hudu na bindigar AK-47..”

Sanarwar da SP Kiyawa ya fitar ta ce tuni bincike ya kankama a kan lamarin.

Idan za a iya tunawa, ko a ranar Talatar da ta gabata sai da aka sami fashewar wani abu da ake zargin bam ne a kusa da wata makaranta da ke unguwar Sabon Gari a cikin birnin na Kano, inda aka samu asarar rayuka tara, wasu kuma suka jikkata.

Sai dai a lokacin, ’yan sanda sun tsaya kai da fata cewa wata tukunyar gas ce ta fashe a shagon wani mai walda, ba harin bam ba ne.