✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama matashin da ya kware a satar babura a Gumel

A Lahadin da ta gabata ’yan sanda sun kama wani matashi a Gumel da ya kware wajan satar babura yana sayar da su a Jihar…

A Lahadin da ta gabata ’yan sanda sun kama wani matashi a Gumel da ya kware wajan satar babura yana sayar da su a Jihar Bauchi. Matashin mai suna Musa Yakubu, dan asalin kauyen Maigatari, dan kimanin shekara 23.

Kakanin rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar al’amarin. Ya ce sun kama matashin a daidai lokacin da yake kokarin yi wa wanda ya dauka hayar wayo, cewa sun yi mantuwa a baya, don haka ya ba shi babur din domin ya koma ya dauko. Shi kuma mai babur ya sanar da ’yan sanda halin da yake ciki.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, barawon baburan ya ce wannan shi ne karo na biyu da ya saci babura ta hanayar dabara, inda yake amfani da kananan yara wajan yaudarar masu babur, ya bar su da yaran ya tsere da babur dinsu.

Ya kara da cewa idan ya saci babur, ana ba shi Naira dubu ashirin ne komai kyansa. Ya ce yana yin wannan hali ne saboda iyayensa sun rasu sun bar shi, shi kuma ba shi da wani gata da zai iya daukar nauyin karatunsa, shi ne ya sa yake satar baburan yake sayarwa.

Kakakin ’yan sanda ya ce yanzu haka sun dukufa wajen damke duk wadanda suke da hannu ciki, wajen hada baki da yara suna sace wa mutane babura a yankin Gumel da Maigatari da babura da Sule Tankarkar domin su gurfanar da su gaban shari’a.