✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama matashi kan zargin satar Naira miliyan 120

An gano abubuwa da dama a hannun wanda ake zargin da suka haɗa da: Keke NAPEP guda 8, Naira miliyan 35 tsabar kuɗi da Gine-gine…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta kama wani matashi mai shekara 34 mai suna Glory Samuel bisa zargin damfarar wani fitaccen ɗan kasuwa har Naira miliyan 120.

Bayanin haka na ƙunshe ne a sanarwar da Kakakin Rundunar, SP Ahmed Mohammed Wakil ya raba wa manema labarai a Bauchi.

Sanarwar ta ce, an kama wanda ake zargine saboda, “Koken da mai kuɗin ya kai ga ’yan sanda a ranar 1 ga Afrilu, 2024, yana zargin cewa an cire kuɗi sama da Naira miliyan 2 da dubu 68,000 daga asusun bankin kamfaninsa.”

Ya ce, “Kan haka ne Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Auwal Musa Mohammed, ya ba da umarni ga Sashen Binciken Sirri ya binciki lamarin ba tare da ɓata lokaci ba.

Sanarwar ta ce binciken da suka yi ya nuna cewa wanda ake zargin ya cire maƙudan kuɗi har Naira miliyan 120 a asusun bankin mai ƙarar ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce, “A yayin da ake yi masa tambayoyi, Glory Samuel ya amince cewa ya ci amanar maƙwabcinsa, wanda ya kai ƙarar, wanda suka yi tarayya da shi a kasuwa na sama da shekara 15.”

Samuel ya ce wani abokinsa da suka haɗu a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Tarayya

da ke Bauchi a shekarar 2011, wanda ya samu horon ilimin kwamfuta, ya tabbatar masa cewa zai iya samun kuɗi ta hanyar shiga wayar wani mai hannu da shuni.

Kuma sai Samuel ya ci amanar maƙwabcinsa, ya ci bashi a waya, inda ya bai wa abokin aikinsa damar shigar da kuɗi zuwa asusun bankuna daban-daban, irin su Opay da MoneyPoint a lokuta da dama.

Wakil ya ce, “Bayan binciken da aka gudanar, an gano abubuwa da dama a hannun wanda ake zargin da suka haɗa da:

  1. Keke NAPEP guda 8
  2. Naira miliyan 35 tsabar kuɗi
  3. Gine-gine 2 da ba a kammala ba
  1. Buhu 60 na garwayin girki
  2. Taki buhu 30.
  3. Babura 2.
  4. Kekunan ɗinki na masana’antu guda biyu.

Ya ce, “Wanda ake zargin, wanda salon rayuwarsa ya canza sosai, ya tabbatar wa kawunsa da budurwarsa cewa yana samun kuɗi ne ta hanyar kasuwanci ta Intanet da suka tambaye shi hanyar da yake samun kuɗi.

Sanarwar ta ce Kwamishina Auwal Musa Mohammed, ya buƙaci jama’a su riƙa sa ido tare da tabbatar da tsaron kuɗaɗensu tare da kai rahoto ga ’yan sanda ko su kira:

  • PPRO: 08034844393
  • CRU: 08036392107

ko ta shafin Facebook a UMARNIN YAN SANDA JIHAR BAUCHI ko KOKARIN BAUCHI da Ɗ @crubauchi.