Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta ce jami’anta sun cafke wasu mutane da suka kware wajen sarrafa gurbatacciyar giya da sauran kayayyakin sha na jabu a Fatakwal, babban birinin Jihar.
Kakakin rundunar a Jihar, SP Nnamdi Omoni wanda ya sanar da hakan lokacin da yake bajekolin wadanda ake zargin ranar Litinin.
- Matashi ya daina cin abinci saboda soyayyar ’yar fim, Hadiza Muhammad
- An sake bude kasuwanni 7 a Jihar Zamfara
Ya ce an cafke su ne a gidan da suke aika-aikar, wanda ke kan titin Eligbolo a unguwar Rumuokoro ta birnin Fatakwal.
Nnamdi ya ce mutanen na sarrafa ababen shan da aka yi ittifakin suna da illa kuma za su iya cutar da lafiyar al’umma.
A cewarsa, mutanen da aka kama sun hada da Akhayera Collins da Christian John, yayin da ragowar suka cika wandunansu da iska.
Wasu daga cikin kayayyakin da aka kama daga hannunsu inji kakakin sun hada da giya da wasu lemukan da kuma kwalaben da ake kokarin zuba sinadaran a cikinsu.
Ya ce mutanen sun amsa laifukan da ake zarginsu da su, kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu don su girbi abin da suka shuka.