✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama masu lalata allunan ’yan siyasa a Kano

An kama mutanen ne a sassa daban-daban na Jihar

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta yi bajekolin wasu matasa da ta cafke bisa zarginsu da lalata allunan ’yan takara a sassa daban-daban na Jihar.

Matasan dai na cikin cikin mutum 364 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a hedkwatar rundunar da ke Kano a ranar Litinin.

Daga cikin wadanda ake zargin, har da da masu garkuwa da mutane da masu fashi da makami sai wadanda ake zargi da sata da daba da kuma kwace.

A cewar Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Mamman Dauda, rundunar ta sami nasarar ce cikin ’yan kwanakin nan musamman a wajen tarukan wasu jam’iyyu a Jihar.

CP Mamman ya kara da cewa rundunar ba za ta zura idanu wasu mara son zaman lafiya su ci gaba da tayar da fitina da ta’adi da kuma tayar da hankulan al’umma ba.

Mustapha Lawan daya daga cikin wadanda ake zargi da yaudarar wasu mutane da aka sace wa mahaifi wanda ya kira su a waya, bayan ya boye nambarsa har ya bukaci su bashi naira dubu dari kafin ya sake shi.

Wanda ake zargi ya tura musu da asusun banki, kuma an saka masa Naira 40,000.

Shi kuwa wani mai suna Ibrahim Abdullahi Panshekara ya bayyana wa manema labarai cewa sun haura wani gida ne bayan wani ya sanar da su cewa an shigar da Dalolin Amurka, sai dai bayan sun dauko kudin ne aka samu nasarar kama su.

Hamisu Abdu Danzaki kuwa, ya shaida wa manema labarai yadda ya shirya yaudarar wasu mutane da aka sace wa mahifi,wanda ya yi alkwarin yin addu’a bayan ya karbi kudade a hannunsu sama Naira miliyan biyar, amma ba a yi addu’ar ba.

A karshe rundunar ta ce da zarar ta kammala gudanar da bincike za ta gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci daidai da laifukan da ake zargin su da aikatawa.