✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama masu ƙwacen waya 985 a Kaduna

Waɗannan nasarorin wani ɓangare ne da ke nuna ƙwazon aiki da jajircewar ‘yan sanda a Jihar Kaduna.

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce an kama wasu mutane 985 da ake zargi da ƙwacen wayar salula da masu fashi da makami 73 da kuma masu garkuwa da mutane 70 a Jihar Kaduna cikin watanni biyu da suka gabata.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna, Ali Dabigi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da gudana a ranar Alhamis a Kaduna.

Dabigi ya yaba wa wasu muhimman mutane da cibiyoyi da goyon bayansu kan taimaka wajen nasarorin da aka samu a cikin watanni biyu da suka gabata.

“A cikin watanni biyun da suka gabata, an kama mutane 985 da ake zargin masu ƙwacen waya ne, da 73 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da kuma masu garkuwa da mutane 70, yayin da aka kashe ‘yan fashi tara.

“Mun kwato bindigogin AK 47 guda biyar; da 7 makamai ƙirar gida; harsashe 1,817; an kuma ƙwato motoci takwas iri daban-daban, yayin da aka kama mutane takwas da ake zargi da laifin satar mota.

“Motoci bakwai nau’uka daban-daban; An kuma ƙwato babur guda ɗaya da shanun sata 29, yayin da aka kama ɗaya da ake zargin ɗan fashin jirgin ƙasa ne.

“Waɗannan nasarorin wani ɓangare ne da ke nuna ƙwazon aiki da kuma jajircewar da jami’an ‘yan sanda a Jihar Kaduna suke yi.

“Muna ci gaba da jajircewa wajen yi wa al’ummar jihar Kaduna hidima tare da kare mutuncinsu da ƙwarewa,” in ji shi.