Wani abun al’ajabi ya faru a kasar Uganda inda jami’an tsaro suka rika bi suna cafke magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.
BBC ya ruwaito cewa, akalla magoya bayan Arsenal takwas aka kama a birnin Jinja na kasar, sakamakon murnar nasarar da kungiyar ta yi kan babbar abokiyar hamayyarta Manchester United a wasan Firimiyar Ingila da suka buga ranar Lahadi.
Magoya bayan – wadanda ke sanye da jajayen rigunan kungiyar – na rike da wani abu da ke alamta kofin Firimiyar.
’Yan sanda sun ce mutanen ba su da izinin gudanar da gangamin, kuma yin hakan laifi ne a kasar.
’Yan sanda sun kama magoya bayan – wadanda ke cikin jerin gwanon motoci ranar Litinin da safe – inda daya daga cikinsu ke rike da kofin da suka hada kudi suka saya a wani shago a kasar.
Arsenal dai ta samu nasara a kan abokiyar hamayyarta Manchester United da ci 3-2 a wasan na ranar lahadi.
Sakamakon ya bai wa kungiyar tazarar maki biyar a saman teburin Firimiyar Ingila, lamarin da ya bai wa magoya bayanta a fadin duniya kwarin gwiwar daukar kofin karon farko cikin shekara 19.