✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun kama barayin yara a Bauchi

Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta samu nasarar kama wasu mutum hudu bisa zarginsu da sace wani yaro dan shekara bakwai mai suna Yunusa Musa.Kakakin…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi ta samu nasarar kama wasu mutum hudu bisa zarginsu da sace wani yaro dan shekara bakwai mai suna Yunusa Musa.
Kakakin rundunar, DSP Haruna Mohammed ne ya bayyana wa manema labarai kama mutanen masu suna danladi Abdullahi da Alhaji Mohammed Ali da Abubakar Ibrahim da wata mace da ba a bayyana sunanta ba, wadanda aka kama a bayan Kwalejin Kimiyya da kere-kere na Abubakar Tatari Ali da ke hanyar Jos.
An ce mutanen sun zo daga Zariya ne, amma aka kama su suna aikata mumunan aiki, inda daliban makarantar suka ba su kashi suka kuma kone motarsu da aka samu da Naira dubu 177 da 555 da wayoyin salula biyar da alawa da biskit iri-iri a ciki.
daliban da abin ya faru a kan idonsu, sun ce mutanen sun yanka yara biyu da suka fito da su daga cikin motarsu kirar Honda Hennesee, wani dalibi ne da ya biyo dajin daga Kwalejin Aikin Gona ta Yalwa ya hange su ya kuma ankarar da daliban inda suka yi musu dirar mikiya suka kone motar suka yi musu dukan kawo wuka kafin su mika su ga jami’an tsaro.
daliban sun ce akwai kudi mai yawa da kaya a cikin motar da yara biyu da suka yanka da daya da ba su kai ga yanka shi ba, jami’an tsaro sun tafi da su. DSP Haruna Mohammed ya ce an mika su ga sashin binciken manyan laifuffuka na rundunar don ci gaba da bincke.

%d bloggers like this: