✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun harba wa Sowore ‘tiyagas’

’Yar sanda ta harbi mawallafin jaridar Sahara Reporters da tiyagas a wurin zanga-zanga

’Yan sanda sun harbi mawallafin jaridar intanet ta Sahara Reporters, Omoyele Sowore a Abuja.

Lauyan Sowore, Inibehe Effiong, ya ce wata ’yar sanda ce ta harbe shi a safiyar Litinin, da hayaki mai sanya kwalla a yayin wata zanga-zanga.

“Wata ’yar sanda ce ta harbi Omoyele Sowore a daidai Unity Fountain a Abuja, an kuma kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.

“Kai tsaye ta harbe shi da kurtun hayaki mai sanya kwalla a cinyarsa ta dama. Sowore aka nufa kai tsaye,” a cewarsa.

Karin labarin na tafe..