Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta hana yunqurin fasa wani shago da wasu vata-gari suka yi qoqarin yi a Unguwar Buba Shongo da ke cikin birnin Gombe, inda ta qwato wani babur da kayan da ake zargin an yi niyyar amfani da su wajen fasa shagon.
A cewar sanarwar da mai Magana da Yawun Rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, lamarin ya faru ne da misalin qarfe 3:00 na safiyar Litinin, 1 ga Watan Yuli, 2025, lokacin da jami’an Operation Hattara ke kan sintiri a daren.
Jami’an sun hango wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suna qoqarin fasa wani shago mallakin wani Muhammadu Adamu Musa, mai shekara 42 da haihuwa.
Da vatagarin suka hango motar sintirin ‘yan sanda na qaratowa, sai suka tsere suka bar shagon ba tare da cimma burinsu ba.
Kayan da aka samu a wurin sun haxa da baqin babur qirar Yamaha mai lamba GME 480 VN da wani qarfe na tanqwara qoafa da takalmin roba guda xaya.
“Dukkan kayan da aka qwato suna hannun ‘yan sanda, kuma bincike yana ci gaba a kan zargin haxa baki da yunqurin aikata laifi,” in ji sanarwar.
Rundunar ta bayyana cewa wannan lamari ya qara tabbatar da cewar dokar da ta takaita zirga-zirgar babura a cikin dare a faxin jihar na nan daram, domin yawan laifukan da ake aikatawa da su a wannan lokaci na dare.
Rundunar ta kuma tabbatar wa da jama’a cewa tana ci gaba da qoqari don kamo waxanda suka gudu tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
Haka zalika, rundunar ta buqaci jama’a da su kasance masu lura da abin da ke faruwa a muhallansu tare da ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma