Baltasar Engonga Ebang, mutumin nan dan kasar Equatorial Guinea da a bara ya saki bidiyon lalatarsa da mata sama da 400 na fuskantar shari’a a kotu kan badakalar kudade.
Baltasar, wanda tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa ta kasar Equatorial Guinea ne dai an gurfanar da shi a gaban kotu ne bisa zargin karkatar da kudade a karkashin Ma’aikatar Kudin kasar.
Masu shigar da kara na neman a yanke masa hukuncin daurin shekara 18 a kurkuru sannan a umarce shi ya dawo da wasu kudaden masu yawa.
- ’Yan Najeriya sun fara begen Buhari saboda azabar TIinubu – Amaechi
- Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota
Ana dai zarginsa ne da almundahana, azurta kai da kuma rub-da-ciki a kan dukiyar al’umma lokacin da yake rike da mukamin hukumar.
Lauyoyi masu shigar da kara na zargin Baltasar da yin babakere a kan kudi har sama da CFA biliyan daya, kwatankwacin sama da Naira biliyan biyu da rabi.
Bugu da kari, lauyoyin na kuma son a yanke masa hukuncin shekara takwas kan laifin almundahana, shekara hudu da wata biyar kan laifin azurta kai, sai kuma shekara shida kan laifin cin amanar ofishinsa.
Lauyoyin sun kuma bukaci kotun ta ci Baltasar tarar CFA miliyan 910 sannan a haramta masa rike kowanne irin ofishin gwamanti na tsawon lokacin da zai shafe a dauren.
To sai dai lauyoyin wanda ake karar sun yi fatali da dukkan laifukan da ake zargin wanda suke karewa da aikatawa da ma sauran wadanda ake zargin, inda suka ce bas u da tushe.
A watan Disambar bara ne dai bidiyoyin Baltasar na lalata da mata sama da 400 suka cika shafukan sada zumunta. Daga cikin matan da aka gan shi yana lalata da su har da matan ministotin kasar.